<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>23</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Ranan nan da ka bayar ta faɗi,
 Kai ne ka sa duhu ya yi.
 Mu rera waƙoƙi gare ka,
 Yabonka kuwa zai tsarkake mu.

[V2]
 2) Mun gode don Ekklesiyarka,
 Da himma ta ke shaidarka,
 Tana kuwa kiwon dukan duniya,
 Ba ta da hutu, ko kaɗan.

[V3]
 3) A ƙasashen duniya dayawa,
 Hasken safe 'na ƃullowa,
 Addu'a ba ta fasawa,
 Yabo gare ka kullayaumin.

[V4]
 4) Loton da mu ke barci fa,
 Waɗansu su ke farkawa,
 Kowane lokaci, ƴaƴanka
 Yabonka su ke furtawa.

[V5]
 5) Mulkinka ba zai shuɗe ba
 Kamar su mulkokin duniya,
 Amma ya tabbata da iko,
 Har kowa ya bi nufinka.</lyrics>
<title>Ranan Nan da Ka Bayar Ta Faɗi LW23</title>
</song>